Gwamnatin Jihar Kano ta ce zata kafa wani Kwamiti na masana da zai tattara tarihin sabbin Masarautun da aka dawo da martabarsu, domin alkinta tarihin don Amfanin al’umma.Kadaura24 ta rawaito Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan yayin da ya ziyarci Fadar Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya a Juma’ar nan.Gwamna Ganduje yace Samar da tarihin Masarautun zai sa Sauran al’ummar duniya su san Cewa Masarautun Suna da tarihin da ya kamata a girmama su saboda shi.Ya bukaci Sarkin na Gaya daya Fara tattara duk abun da ya Sani game da tarihin Masarautar ta Gaya, domin nan gaba kadan za a kafa Kwamitin tare da Kaddamar da shi domin fara aikinsa.Gwamna Ganduje ya bada tabbacin Gwamnatin Kano zata cigaba da Kai aiyukan Raya Kasa da cigaban al’umma Masarautar ta Gaya domin Cika burin Gwamnatin na Samar da Kananan burane a Jihar Kano.Gwamna na Kano ya kuma roki al’ummar sabbin Masarautun da su Maida hankali wajen tallafawa yunkurin Gwamnati na bunkasa Masarautun, ta yadda Masu ikirarin zasu rushe Masarautun baza su iyaba ko da sun Sami dama.A yake nasa Jawabin Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya ya yabawa Gwamna Ganduje bisa aiyukan Raya Kasa da cigaban al’umma a Masarautar ta Gaya don Kara inganta ta.Mai Martaba Sarkin ya Kuma ce ita ma Masarautar tana nata kokarin wajen Ganin an Samar da tituna futilun hanya da Sauran abubuwan da zasu Kara bunkasa Masarautar.

Murtala Sule Garo yafi kowa Cancantar Zama Mataimakin Gwamnan Kano.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rufe karɓar biyan kuɗin Hajji na shekarar 2026.
TARON KOYAR DA KIWON KAJI DA KIFI: KPA
Dalung yayi Alhinin halin da Nigeria ke Ciki .
Manoma sun Kira ga Gwamnati Tarayya tayi taka Tsan-Tsan
Gwamna Peter Mbah na Enugu ya koma jam’iyyar APC
CP Bakori Extends Strategic Engagement to Wudil Area Command, Reaffirms Intelligence-Led Policing
AIG Ahmed Pledges Support for Kano Safe Corridor Programme
Arewa Consultative ACF Endowment Fund Sets Bold Agenda for Transparency, Education, and Empowerment
BATTLE OF THE TITANS: CAN MUHAMMAD GARBA CONFRONT IBRAHIM WAIYA – “THE RAVE OF THE MOMENT?
Kano Govt Suspends Official Over Vandalisation of Facilities
Governor Radda Launches Statewide Annual Livestock Vaccination Exercise Across 361 Wards